14 Mayu 2019 - 17:02
Musulmai Na Zaman Fargaba A Sri Lanka

Sojoji a kasar Sri Lanka suna ci gaba da sintiri a garuruwan da masu kin jinin musulmi suka fara kai masu farmaki a gidaje da wuraren aikinsu don daukar fansar hare-haren ta’addanci ta daren easter wadanda suka lakume rayukan mutane kimani 250 a coci-coci, da wani hotel a birnin Colombo babban birnin kasar a cikin watan da ya gabata.

A ranar Lahadin da ta gabata ce wasu jama’ar gari suka fara bin gari-gari suna ta kai farmaki a kan gidaje da wuraren aiki da shaguna na musulman kasar, inda ya zuwa yanzu dai rahotannin sun bada labarin cewa an dabawa mutum guda wuka har ya kuma ya mutu sanadiyyar hakan.

Sannan an kai hare-hare kan masallatayya da kuma kokkonan alkur’ani a wasu garuruwa a kasar.

Mafi yawan musulmi dai sun sami mafaka ne ko a masallatayyan kasar inda jami’an tsaro suke hana mutanen gari shiga, ko kuma a cikin gonakin shinkafa a bayan gari don tsara da rayukansu.

A garin Kottapitiya mafi yawan musulmi sun bar gidajensu da kuma wuraren sana’arsu zuwa masallaci.

Shugaban kasar ta Sri Lanka dai ya bawa yansanda damar hana duk wani farmakin ramuwar gayya kan musulman kasar sanadiyar harin na watan da ya gabata.

Yawan musulmi a kasar Sri Lanka ya kai kashe 10% na mutane kasar miliyon 22.